5 Mayu 2022 - 21:33
Kungiyar Hamas Ta Gargadi Isra’ila Game Da Mamaye Masallacin Kudus

A cikin wata sanarwa da Kungiyar gwagwarmayar musulunci Ta hamas ta fitar a jiya laraba, ta jaddada matsayinta na ci gaba da kare masallacin kudus ta kowanne hali daga mamaya da kotsen sojojin Gwamnatin yahudawan sahyuniya kuma sun yi kira ga alummar falasdinu da su mamaye masallacin kudus .

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - Kungiyar ta Hamas ta yi kira da babbar murya ga dukkan falasdinawa da su yi wa masallacin kudus zobe a gobe juma’a idan Allah ya kaimu domin dakile makircin isra’ila na daga tutarta da rera taken Haramatacciyar kasar a masallacin kudus mai alfarma

Ana tana bangaren itama kungiyar Fatah ta bukaci falasdinawa das u yi zaman dirshan a harabar masallacin Kudus a gobe juma’a domin dakile makircin da isra’ila take kullawa na mamaye masallacin mai alfarma,

Daga karshe ta jaddada matsayinta na ci gaba da yin fito-na fito da sojojin Isra’ila game da hare-haren da suke kaiwa a birnin Kudus jenin .

342/